An bayyana wata mata mai suna Anna Qabale Duba yar asalin kasar Kenya a matsayin matar da tafi cancanta da cin makudan daloli har Dalar Amurka 250,000 a gasar da aka gudanar a hadaddiyar daular larabawa.
Anna ta sami nasarar ne sakamakon jajircewarta a fannin yaki da yiwa mata kaciya a kasar Kenya.
Bayan cin kyautar ta ta Anna ta sami kwarin guiwa da har ta kaddamar da gidauniyar wayar da kan mata domin yaki da yiwa mata kaciya.