Tawagar Wike, Wasu Gwamnonin PDP Hudu Sun Yi Barazanar Watsi da Atiku a 2023
Daga cikin gwamnonin akwai Godwin Obaseki na jihar Edo da Ahmadu Fintiri na jihar Adamawa
Rikicin da na jam’iyyar PDP ya buɗe sabon shafi yayin da karin wasu gwamnoni hudu suka yi barazanar kauracewa ɗan takarar shugaban ƙasa, Atiku Abubakar. A rahoton jaridar The Nation, gwamnonin sun yi barazanar cewa zasu fice daga tawagar kamfen Atiku idan har aka amince da bukatar murabus ɗin shugaban PDP na ƙasa, Iyorchia Ayu.
Gwamna Nyesom Wike na jihar Ribas da ‘yan tawagarsa sun bukaci Ayu ya sauka daga mukaminsa a matsayin sharaɗin da zai sa su mara wa takarar Atiku baya a 2023.
- A cewar tsagin Wike, babu adalci ko kaɗan ɗan takarar shugaban ƙasa da shugaban jam’iyya na kasa baki ɗaya su fito daga yanki guda.