Shuhaba muhammadu Buhari ya jajantawa yan kasuwar kantin kwari a kano.
Walid Yusuf Hari
Jawabin jajantawar yazone daga bakin Ministan ayyuka da gidaje Hon Umar ibrahim El-Yakub a ranar asabar a wata ziyara daya kai dan jajantawa yan kasuwar ta kantin kwari bisa iftila’in ambaliyar daya samemu a makon daya gabata.
Ministan ya kuma yaba da yadda yan kasuwar suka tashi tsaye dan magance faruwar hakan anan gaba, yakuma bayyana takaicinsa bisa yadda wasu yan kasuwar suke gine-gine akan magudanan ruwa, inda yai kira da adakatar da irin wadannan gine-gine kuma hukumomi su dinga sanya idanu yayin da za’ayi gini.