Shugaban kasar China, Xi Jinping, ya bayyana a cikin wani jawabi da ya gabatar a shekarar 2021 cewa, “Ko kasa na da dimokuradiyya ko a’a ya kamata al’ummar kasar su ne su tantance hakan, ba wai wasu ‘yan tsiraru daga waje su tilasta ra’ayinsu ba.”
Ya kara da cewa, “Ya kamata al’ummar kasa da kasa su amince da ko wata kasa na tafiyar da dimokuradiyya, ba wai wasu ‘yan alkalai da suka nada kansu su rika yanke hukunci bisa son ransu ba.”









