An bukaci yan Majalisun tarayyar Najeriya da su hakura su Rufe majalisar kowa ya koma gida tunda sun kasa Samar da sassauci GA yan kasar da hada kan Najeriya.
Bukatar Hakan ta fito ne daga Sanata Smart Adeyemi a jawabin da ya gudanar a gaban majalisar dattawan Najeriya.
Adeyemi yace yan Najeriya mafi yawan su suna cikin talauci da kuncin rayuwa wanda hakan ke nuna majalisar ta gaza ainun gara ma ace rufeta aka yi kowa ya koma gida.
Ya Kara da cewa kasar ta zama sansanin zubar da jini da rashin kwanciyar hankali ta kowanna bangare kama daga Arewa maso yamma da Arewa maso gabas da kudu maso yamma da kudu maso kudu.
Adeyemi a cikin harshen Ingilishi da shaukin talauci yace ‘Shut down the national assembly, let us go home. Nigeria has collapsed’ – Sen. Smart Adeyemi cries out…