Masu garkuwa da mutane sun ja kunnen gwamnatin tarayya

Cikin wani faifan vidiyo da yake kewayawa anga yan taadda sun saki wani dattijo sakamakon tsufa da yayi ainun.

 

Sai dai kafin sakin mutumin yan taaddan suna mika sakon gargadi ga gwamnatin tarayya kan cewa tayi gaggawar shirya zama domin tattaunawa da su inda zata biya musu bukatun su.

 

A lokuta da dama yan taadda sukan karbi kudin fansa ne a duk lokacin da suka sami nasarar kwasa ko yin garkuwa da wasu mutane,  sai dai a wannan karo sunce ba kudi ne damuwar su ba.

 

Kazalika sunce wannan ba komai bane in har gwamnati ta gaza biya musu bukatun su.

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
guest
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments