Hukumar Nigeria Centre for Disease Control (NCDC) na aiki kafada da kafada da hukumomi a Jihar Cross River bayan tabbatar da samun wani sabon mai ɗauke da cutar COVID-19.
Babban Darakta Janar na hukumar, Dr Jide Idris, ya shaida wa Kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya (NAN) a ranar Talata a Abuja cewa hukumar ta riga ta kunna dukkan matakan gaggawa domin dakile yaduwar cutar.
Rahoton NAN ya nuna cewa Ma’aikatar Lafiya ta Jihar Cross River ta tabbatar da bullar cutar ga wani ɗan ƙasar waje mai shekaru 53, wanda ya fara nuna alamun cutar makonni bayan isowarsa Najeriya, sannan aka tabbatar da kamuwarsa da cutar a University of Calabar Teaching Hospital.












