Adadin wadanda suka mutu sakamakon kamuwa da cutar kwalara ya karu zuwa 382.
Rahoton Cibiyar Yaki da Cututtuka masu yaduwa na NCDC) ya bayyana cewa cutar kwalara ta barke a jihohi daban-daban na kasar nan, bayan ambaliyar ruwan da ya yi kamari sakamakon mamakon ruwan sama.
A cikin wata sanarwa da hukumar ta saki ta bayyana cewa, mutane dubu 11 da 820 ne aka tabbatar sun kamu da cutar kwalara tun daga watan Janairu, kuma adadin mutanen da suka rasa rayukansu sakamakon annobar ya karu zuwa 382.