Wata motar haya mai kirar bas dauke da fasinjoji 18 ta kama da wuta a yayin da take tsaka da tafiya da su.
Lamarin dai ya faru ne a kauyen Komo Araromi da ke kan titin Ajase Ipo a Jihar Kwara, sai dai an auna arziki fasinjojin sun tsallake rijiya da baya.
Motar bas din da ibtilain ya ritsa da ita mai kirar Hiace ce, kuma ta taso ne daga Oshogbo ta Jihar Osun, kwatsam sai ta kama wuta.
Kazalika an yi sa’a daukacin fasinjojin motar sun fice daga cikinta a kan lokaci, babu wanda ransa ya salwanta.
Kwamandan Hukumar Kiyaye afkuwar Hadura ta Kasa FRSC reshen Jihar Kwara, Jonathan Owoade, ya tabbatar wa manema labarai da faruwar lamarin.
Owoade ya ce wutar ta kama ne sakamakon yoyon man fetur da motar take yi, hakan ne ya sa ta kama da wuta