An bukaci mutane musamman Wadanda suke da sani da yarda da cewa Allah subhanahu wataala zai tashe su aranar da yake so yayi musu hisabi, da kada su Bata lokacin su wajan neman yardar wani mahaluki ba Allah da ya halicce su ba.
Bukatar hakan ta fito nee daga bakin babba malamin addanin musulunci Sheikh Ismail Menk.
Shehin malamin yace ana so Koda yaushe Mai Imani ya kasance Allah subhanahu wataala shine alkiblar sa da dukkan manufofin sa domin ya samu damar Gina rayuwa Mai inganci a Rana gobe.
Kazalika ya ce aduk lokacin da bawa ya Mika wuya ga Allah subhanahu wataala ta hanyar bin manzon tsira s a w to lallai ya hau kan hanya madaidaiciy.