Ana gudanar da babban taron bitar kan yarjejeniyar hana makaman halitta karo na 9 a babban ginin MDD dake birnin Geneva na kasar Switzerland.
A jiya Talata, jami’ar Tianjin da ma’aikatar harkokin wajen kasar China sun shirya wani taron hadin gwiwa kan takardar ba da shawara ta Tianjin dangane da ka’idojin da masana kimiyya suke bi a harkokin tsaro masu nasaba da illolin da nazarin halittu ke haifarwa ga dan Adam da muhalli.
Shugaban tawagar Sin dake halartar babban taron kuma jakadan Sin mai kula da harkokin kwance damara, Li Song, ya bayyana cikin jawabinsa cewa, masana kimiyya daga kasashe fiye da 20 ciki har da kasar Sin, sun fito da takardar ta Tianjin ga al’ummomin duniya, wadda ta dace da yanayin da muke ciki, kuma ta bayyana yadda masana kimiyya daga kasashe daban daban suke inganta hadin gwiwarsu a harkokin tsaro masu nasaba da illolin da nazarin halittu ke haifarwa dan Adam da muhalli, yayin da ake fama da annobar cutar sarke numfashi ta COVID-19.
Jami’in hukumar dake goyon bayan aiwatar da yarjejeniyar hana makaman halitta, ya bayyana cewa, takardar, ta kasance a matsayin abin koyi ga masana kimiyya na duniya sun taka rawar gani a yarjejeniyar hana makaman halitta. An riga an yi tattaunawa kan takardar an kuma amince da ita sosai.
Haka zalika, wakilai daga kasashen Pakistan da Brazil, da Rasha, da Philippines da Cuba da sauran kasashe, sun bayyana goyon bayansu ga “Tianjin Guidelines”, sun kuma yaba da rawar da kasar Sin take takawa. Haka kuma sun yi kira ga babban taron bitar yarjejeniyar hana makaman halitta karo na 9, da ya mayar da “Tianjin Guidelines” a matsayin muhimmin sakamakon taron