Wani kwamandan Boko Haram da ya mika wuya mai suna Mallam Adamu Rugurugu, ya bayyana dalilin da yasa ya ajiye makaman yakinsa. Rugurugu ya bayyana cewa ya yanke shawarar fitowa daga jeji tare da mayakansa da dama saboda roko da shiga lamarin da Gwamna Babagana Zulum na jihar Borno ya yi.
Tsohon kwamandan na kungiyar Boko Haram ya bayyana cewa ya zauna ya yi wa kansa wa’azin ta nutsu bayan ya gano cewa abun da yake aikatawa ba daidai bane Rugurugu wanda ya samo sunansa daga filin daaga ya kuma ce ya ajiye makamansa ne saboda Gwamna Babagana Zulum da ya shigo lamarin Rugurugu ya bayyana cewa ya yanke shawarar fitowa daga jeji tare da mayakansa da dama saboda roko da shiga lamarin da Gwamna Babagana Zulum na jihar Borno ya yi, Ku tuna cewa dakarun soji sun kai zafafan hare-hare ta sama da kasa a wuraren mayakan Boko Haram da ISWAP lamarin da ya tursasa su ajiye makaman yakinsu da kuma mika wuya ga dakarun Operation Hadin Kai. Da yake magana a sansanin da aka ajiye fiye da yan ta’adda 14,000 da suka mika wuya tare da iyalinsu a Maiduguri, Rugurugu ya ce ya samu sunansa ne daga ayyukansa a filin daaga yayin da suke arangama da dakarun gwamnati.
An dai fitar da Rugurugu daga cikin jerin yan ta’adda masu taurin kai saboda nasarar da aka samu wajen tattaunawa da shi. Haka kuma ya taimaka wajen lallashi mayaka da dama don su mika makamansu, yana mai basu tabbacin cewa da gaske gwamnatocin tarayya da jiha suke game da karbarsu.