Kungiyar ISWP ta dauki alhakin kai harin jihar Ondo

Gwamnatin Tarayya ta bayyana  mayakan ISWAP da ke kai hare-hare a yankunan arewacin kasar a matsayin wandanda  suka kai kazamin hari a Cocin  Katolika dake Owo a Jihar Ondo wanda yayi sanadiyar mutuwar mutane akalla 40.

Ministan Cikin Gida Rauf Aregbesola ne ya bayyana haka bayan taron majalisar tsaron kasa da ya gudana a fadar shugaban kasa dake Abuja.

Aregbesola yace gwamnati tayi nasarar gano wadanda suka kai kazamin harin ta’addanci, kuma ‘yayan wannan haramcaciyar kungiyar ce ta ISWAP wadda ta dade tana kashe mutane a arewacin Najeriya.

Ministan wanda ya gana da manema labarai tare da Sufeto Janar na Yan Sanda Alkali Usman Baba yace tuni aka baiwa hukumomin tsaron kasar umurnin farautar maharani domin ganin sun fuskanci hukunci.

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
guest
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments