Gwamna Badaru na jihar Jigawa ya bada umarnin rufe makarantu a fadin jihar.
Kwamishinan Ilimi na jihar Dakta Lawan Yusuf shine ya tabbatar da hakan ga manema labarai a birnin Dutse.
Yusuf yace an dauki matakin ne biyo Bayan rahoton sirri da aka samu na yuwuwar Kai hare-haren taaddanci a fadin kasar nan musamman a jihohin da suke da kusanci da Iyakokin ketarawa kasashen ke tare.