Kiristoci sun fitar da sunan wanda zasu zaba a zabe shugaban kasa.

Fasto Samuel Oladele wanda shi ne shugaban cocin Christ Apostolic Church (CAC) na Duniya ya ankarar da kiristoci a game da zabe mai zuwa.

Wani rahoto da Sun ta fitar a ranar Alhamis, ya nuna cewa Fasto Samuel Oladele ya halarci taron Fastoci na shekarar  shekara da cocinsa na CAC ya shirya.

A wajen wannan taro da aka yi a sansanin Ayo Babalola Memorial International Miracle da ke jihar Osun ne malamin addinin ya yi kira ga mabiyansa.

Samuel Oladele yace zabe mai zuwa ba abin wasa ba ne, dole kiristoci su tashi tsaye wajen ganin sun kada kuri’a a kan abin da ya shafi lamarinsu. Sai Kiristoci sun tashi-tsaye

“Dole ne mu maida hankali a kan zabe mai zuwa, ba za ta yiwu muyi wasa yayin da ake daukar matakan da suka shafi addinin must ba.

Ya kuma ce “Ina mai fada da babban murya cewa sha’anin addini da lamarin Yesu ya fi komai muhimmanci.” – Samuel Oladele

Legit ta ruwaito cewa an soki tikitin Musulmi da Musulmi na APC a taron bana mai taken: “Growing in the Grace and Knowledge of the Lord.”

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
guest
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments