An bude asibitin “Turkish Hospital” na farko da ’yan kasuwa na Türkiye suka gina a birnin Misrata na kasar Libiya.
Asibitin galibin likitoci Turkawa za su yi aiki, kuma Anasa Ray zai yi fice tare da ababen aiki na fasahar zamani wajen gano cututtuka da yin magani.
An gina Asibitin mai bangarori 13 da dakunan tiyata 4 kuma an samar da Gadaje 120 na kwantar da marasa lafiya
A cikin kashi na farko na asibitin, akwai bangaren tiyata na zuciya da jijiyoyin jini, cututtukan zuciya, cututtukan da suka shafi kashi, bangaren da ya shafi kwakwalwa, babbar tiyata, bangaren da ya shafi haihuwa da mata, bangaren yara, bagaren daukar hoton jiki, bangaren ilimin sinadiran abinci da sabis na gaggawa.
Asibitin “Turkish Hospital” zai yi jinya ga dubban ‘yan kasar Libiya da ke da bukata.