An bayyana Huldar da ke tsakanin kasar China da Najeriya na kara samun bunkasa a shekarun baya-bayan nan, kuma sassan biyu na kara amincewa da juna ta fuskar siyasa, da hadin gwiwa ta fuskar tattalin arziki, kuma lamarin ya haifarwa jama’ar su da mai Ido
Jakadan kasar China a Najeriya Cui Jianchun, ne ya bayyana hakan a wani taro da aka gudanar a Abuja.
Baya ga haka kuma, kasashen biyu suna kyautata juna ta fuskar tsaro tsakanin kungiyoyin kasa da kasa, tare da yin mu’amalar al’adu a tsakaninsu.
Ya ce kasar Sin na son ci gaba da aiwatar da manyan tsare-tsaren ci gaba da bunkasa 5GIST tsakaninta da Najeriya, bisa ra’ayi daya da shugabannin kasashen suka cimma.
Mahalarta taron sun yaba da huldar da ke tsakanin Sin da kasashen Afirka, sun kuma amince da manyan nasarorin bunkasuwa da kasar Sin ta cimma, karkashin shugabancin Jam’iyyar Kwaminis ta kasar Sin. A ganinsu, shawarwarin da shugaban kasar Sin Xi Jinping ya gabatar dangane da bunkasar duniya da tsaron duniya, da kuma yadda ya jaddada hadin gwiwa a tsakanin Sin da Afirka, a yayin taron ministoci karo na 8 na dandalin tattaunawar hadin gwiwar Sin da Afirka, sun kara hadin kai a tsakanin bangarorin biyu zuwa mataki na gaba.
An kafa dandalin tattaunawar Abuja a shekarar 2018, wanda kwalejin nazarin Afirka ta jami’ar horar da malamai ta Zhejiang, da cibiyar nazari ta Gusau ta Najeriya suke gudanarwa cikin hadin gwiwa a duk bayan shekaru 2.
A bana, an gudanar da taron karo na 3, wanda ya taka muhimmiyar rawa wajen yin mu’amala a tsakanin kwararru na Sin da Afirka.
Wasu tsoffin jami’an gwamnatoci da kwararru daga Sin, da Najeriya, da Kenya, da ‘yan kasuwa, da ‘yan jarida sun ga dacewar muamala da juna, a fannonin zaman lafiya, da tsaro, da rage talauci, da kawo wa manoma alheri, da sa kaimi kan yin ciniki, da yin kirkire-kirkire da fasahar zamani da dai sauran.