Al’amarin ya faru ne a unguwar gwammaja India al’ummar unguwar suka ga dacewar kaddamar da kwamatin yan sintirin biyo bayan fuskantar matsalolin tsaro da yake addabar su, musamman a yankin kwasarawa.
Anasa bangaren babban baturen yan sanda na karamar hukumar Dala ya yaba da wannan kokari kuma yace wannan tamkar Kara rage masa nauyi aka yi kasancewar a duk lokacin da aka sami matsalar tsaro a fadin karamar hukumar a gunrin sa kadai ake neman baasi. Inset.
kazalika shima D C operation na hukumar vigilantee ta jihar Kano Akibu Dan Lami ya ja hankalin yan sintirin da aka kaddamar da su gujewa aikata laifi da muamala da bata Gari insert
A yayin kaddamar da kwamatin sintirin da babban mataimakin kwamandan vigilantin na jihar Kano Akibu Dan Lami ya kira ofishin da aka bude da kwasarawa salamu alaikum kuma yace zasu sa ido sosai domin kwalliya ta biya kudin sabulu.
Dimbun Al’ummar unguwar ta gwammaja sun nuna jindadin su da samun wannan nasara inda wani daga cikin dattawan yankin kwasarawa insane yace fiye da shekaru 40 suna fatan ganin irin wannan Al’amari amma yau cikin yardar Allah burin su ya cika.