A jiya Juma’a ce hukumar Lafiya ta Duniya ta ce an kawo karshen annobar Covid-19, wadda ta yi sanadin mutuwar mutane da dama tare da wargaza tattalin arziki da sha’anin zamantakewar duniya, sama da shekaru 3 bayan da ta ayyana ta a matsayin annoba
Shugaban hukumar Tedros Adhanom Ghebreyesus ne ya sanar da haka a jiya Juma’a, inda ya yi gargadin cewa har yanzu cutar na nan a matsayin barazana.
Wannan mataki na hukumar Lafiyar na zuwa ne bayan da kwamitin kwararru mai zaman kansa da ta nada a game da wannan cuta ta Covid ya ce cutar ba a bukatar mayar da hankali sosai a kan cutar daga hukumar.
Sai dai a cewar Tedros, hatsarin cutar bai kau ba, inda ya yi kiyasin cewa ta kashe sama da mutane miliyan 20 a fadin duniya, kimanin ninki 3 na mutane kusan miliyan 7 da aka ce ta kashe a hukumanvce.