Gwamnatin Anambra, ta haramta Amfani da mini skirt a fadin jihar

Gwamnatin Jihar Anambra ta haramta Amfani da  gajerun yan tofi ga dalibai a fadin jihar.

Kwamishiyar  Ilimi ta Jihar, Farfesa Ngozi Chuma-Udeh, ce ta bayyana hakan a Awka inda tace  haramcin ya zama dole domin makarantu za su dawo hutu a ranar Litinin

Kwamishinan ta yi tir da sabon yayin da ake yi na saka mini siket a matsayin kayan makaanta kuma ta ce rashin tarbiya ne kuma ba za a amince yan makaranta su rika yin hakan ba.

Ta ce: “A matsayin dalibai ya kamata ka yi shiga tsaf-tsaf, ta nuna halaye masu kyau ba shiga irin ta rashin tarbiya ba yayin zuwa makaranta.

Ta kara da cewa  abin da aka amince shine tsawon unifom ya rufe gwiwa ba ya gaza kai wa gwiwa ba, wanda shine sabon yayin da ke bazuwa a makarantu.”

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
guest
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments