Shugabancin kungiyar ci gaban alummar garin kwasamgwami dake karamar hukumar Gezawa ya bukaci matasan yankunan da su kaucewa shiga bangar siyasa,musamman a wannan lokacin da babban zaben shekarar 2023, dake tafe.
Shugaban matasan yankin karamar hukumar Gezawa Alh Aminu Danjimmai ne,ya bukaci hakan dangane da yadda harkokin zabuka suke karatowa na shekarar 2023.
Alh Aminu yace,kasancewar lokacin zabuka yana karatowa,akwai bukatar kungiyar ta ja hankalin matasan yankunan domin kar su bari wasu yansiyasa su yi amfani da su domin cimma muradunsu a siyasance da kuma,sanyasu a cikin yanayi na damuwa da zai haifar musu da matsaloli a rayuwarsu.
Yace,a duk lokacin da yansiyasa suka samu damar darewa kan mulki ba za su tuna da su ba,daga su Sai ,ya,yensu Sai yanuwan matansu da sauran wadanda suke bukatar su zo kusa da su,Inda yace,ba,a hana matasan yi zabe ba,amma,yakamata su yi karatun ta nutsu wajen sanin wanne ma shugaba yakamata su zaba,domin inganta rayuwarsu a nan gaba.
Aminu yace,an Dade ana ruwa kasa na shanyewa akan alamuran da suka shafi harkokin matasa,da kungiyoyin matasa,kasancewar matasa sune kashin bayan kowacce alumma,dolene a ci gaba da kiraye kiraye akansu wajen kiyayewa shiga ala,amuran da za su sauya rayuwarsu da suka hadar da shaye_shaye da amfani da makamai wajen biyawa wasu bukatunsu,inda ya kara da cewa,jamian tsaro da hukumomi da kungiyoyi suna ta kiraye kiraye a garesu na su kaucewa shiga bangar siyasa, ta kafafen yada labarai da gidajen rediyo da talbijin.
Haka zalika,ya yi kira ga iyaye da su iya kokarinsu domin sauke nauyin daya rataya a wuyansu kasancewar, Allah subahanahu wata,ala Sai ya tambayesu ranar gobe alkiyama,inda yace,iyaye suna da rawar takawa wajen fadakar da yayensu ta hanyoyi da dama su kuma fahincesu tare da kaucewa shiga bangar siyasa.
Daga karshe ya shawarci mahukunta da masu ruwa da tsaki a fannin harkokin siyasa, da su fito da wasu hanyoyi da za su saka matasa akan gwadabe nagari da Sai janye hankalin matasan yankuna daban daban na kasar nan,na hada kai da ake yi da matasa wajen yin magudin zabe a yayin zabe da ma bayan zabe.
Daga karshe Alh Aminu kwasamgwami,ya bukaci alummar kasar nan,da su kasance masu gudanar da addu,oin samun zaman lafiya mai dorewa da samun yalwatar arziki, kasancewar alumma suna cikin wani halin rayuwarsu da damuwa dangane da yadda abubuwa suka yi tsada na rayuwa,inda yace,wannan yanayi da ake ciki yanzu babu wata mafita illa,mu ci gaba da addu,oin samun sauki da zaman lafiya.