Daga Sadiq L Hassan.
An buƙaci a binciki Abba ɗan Ganduje, bisa zargin amfani da motocin gwamnati don yin kamfen.
Jam’iyyar adawa ta NNPP, ta bukaci a gudanar da bincike cikin gaggawa kan zargin karkatar da dukiyar jiha da Abba Abdullahi Ganduje, ɗan gwamnan jihar Kano ya yi.
A wata sanarwa da shugaban jam’iyyar NNPP na jiha, Umar Doguwa ya fitar a yau Alhamis, jam’iyyar ta ce ta gano cewa gwamnatin jihar ta karkatar da motoci sama da 30 mallakar hukumar tattara kudaden shiga ta Kano, KIRS, domin gudanar da yakin neman zaben dan Gwamna Ganduje.
Motocin, a cewar Doguwa, wadanda ke dauke da hoton Abba Ganduje, ana shirin raba su ne ga shugabannin APC na mazabar Rimingado, Tofa, da Dawakin Tofa, domin yin gasa da dan takara Tijjani AbdulkadirJobe, wanda ya raba motoci kusan ashirin ga ƴan jam’iyyar NNPP kwanan nan.”
Doguwa, a cikin sanarwar, ya ci gaba da bayyana cewa, “motocin da ake zargi, an ajiye su ne a harabar jami’ar Maitama Sule ta Kano, ana jiran raba wa ga magoya bayan dan Ganduje, Abba.
Jam’iyyar adawar ta kuma yi Allah wadai da ajiye motocin a harabar jami’ar Yusuf Maitama Sule da ke birnin kano a matsayin saba wa ka’idojin hukumar zabe ta kasa INEC na yakin neman zabe.
“Don haka muna rokon hukumomin yaki da cin hanci da rashawa irin su EFFC, ICPC da INEC da su binciki almundahana da dukiyar kasa, bisa saba wa ka’idojin zabe.
Jam’iyyar ta kuma bukaci masu kada kuri’a a mazabar da abin ya shafa da kuma a fadin jihar da su yi watsi da siyasar son zuciya da cin hanci da rashawa da kuma abubuwan da ba su dace ba.