Shugabancin kungiyar matuka motocin haya ta Kasa reshen jihar Kano,dake railway da Malam Kato sun koka dangane da tashin gwauran zabi
da man fetur da man
Gas suka yi a halin yanzu ya kawo nakasu da koma baya a fannonin sufurin kasar nan,idon aka yi duba da lokutan baya.
Sakataren kungiyar matuka motocin hayar na Kasa reshen railway, Naziru Sani Dandago,ya bayyana haka ga manema labarai dangane da halin da yankungiyoyin biyu suka tsinci Kansu a ciki a harkokin sufuri da kuma,kalubalen dake tattare da sana,arsu.
Daga wakilin mu ibrahim sani gama
Naziru Sani, ya ce,tashin gwauran zabin da man yayi ya shafi harkokin kasuwanci da sufuri da sauran al,amura na Yau da kullum, da suka shafi talakawa kai tsaye,inda ya bukaci Gwamnati a matakai daban daban da su taimakawa fannoni sufuri ta kowanne hali,kasancewar bangaren albarkatun man fetur abune da ya shafi kowa da kowa a fadin kasar nan.
Haka zalika, Sakataren kungiyar yace,kungiyar tana tattarawa Gwamnati kudaden haraji sama da naira miliyan biyar a duk shekara, adon haka yake kira ga Gwamnati kan ta tallafawa masu sana,ar harkokin sufuri ta kowanne hali.
A jawabinsa,tun da farko,daya daga cikin kwamatin Amintattu na kungiyar matuka motocin haya ta Kasa reshen, Malam Kato, kuma, Direba da ya kwashe shekaru arbain yana gudanar da sana,ar Tukin Mota,Malam Bako Shatima,ya bayyana cewa: direbobi suna mutukar fuskantar kalubale a yayin da suke tafiye_tafiye zuwa wasu jihohin kudu da Arewacin Najeriya.
Malam Bako shatima,yace,rashin kyawawan hanyoyi da rashin samun cikakken tsaro na daga cikin abubuwa da suke ci musu tuwo a kwarya,musamman hanyoyin Kaduna da Abuja,Wanda yanzu alummar Najeriya basu da cikakken tabbas dangane da wadannan hanyoyi.
Haka zalika, shatima, ya bukaci Gwamnati da masu Ruwa da tsaki a fannonin tsaro da harkokin sufuri, da su yi duk maiyiyuwa wajen ribanya kakarinsu domin kawo musu daukin gaggawa yadda za su ji dadin gudanar da alamuransu cikin kwanciyar hankali da lumana.