An buɗe guri na farko a duniya da za’a riƙa karɓa gami da tara madarar ruwan nono na mata a California dake ƙasar Amurka. Ƙwararru zasu gwada yiwuwar magance cututtuka da nonon da aka karɓa.
Cibiyar wacce aka buɗe ta a San Diego zata jaraba yin amfani da ruwan nonon matan wajen magance wasu manyan cututtuka da suka haɗa da ciwon zuciya, ciwon suga da kuma sankarar mama.
Darekatan hukumar, Lars Bode ya bayyana cewa akwai likitoci da sauran masu gwaje-gwaje da suka jaraba amfani da ruwan nonon a lokuta da dama a can baya.
Cibiyar na karɓar madarar nonon da mata ke zuwa suna badawa a kyauta kuma Za’a taimaka wa matan da basu iya shayarwa dashi.