Ministan ‘Yan Sandan kasar Africa ta kudu, Bheki Cele ya bayyana rashin fahimtar juna da rikice-rikice da kuma daukar fansa na daga cikin manyan dalilan da ke sanya aikata kisan gillar, a kasar.
Cele ya bayyana hakan a matsayin abin takaici duba da yadda adadin mutanen da ake hallakawa ya karu da kashi 16 da rabi a watanni shida na farkon wannan shekara, kamar yadda alkaluman hukumar suka bayyana.
Ministan ya ce, a shekarar da ta gabata, ana kashe mutane 65 a kowacce rana a fadin kasar Afirka ta Kudu tsakanin watan Janairu zuwa Disamba.
A ranar Larabar da ta gabata, jama’a sun yi wa wasu mutane guda 2 da ake zargin ‘Yan fashi ne kisan rotse, inda suka kashe su da duwatsu, kafin kona gawarwakinsu a arewacin Yankin Limpopo lokacin da suka yi kokarin garkuwa da wata mata.
Cele ya kuma ce, an samu raguwar masu aikata laifin fyade a cikin watanni 6 da suka gabata na wannan shekara, inda aka samu fyade 9,516, abin da ke nuna samun fyade sama da 100 kowacce rana.