Jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP) mai samun goyon bayan Nyesom Wike ta fitar da jadawalin gudanar da zaɓe, tare da sanya kuɗin fam ɗin tsayawa takarar shugaban ƙasa a kan Naira miliyan 51.
A cikin jadawalin da jam’iyyar ta fitar, ta bayyana matakan da za a bi wajen zaɓen ‘yan takara a matakai daban-daban, ciki har da zaɓen fidda gwani na shugaban ƙasa.
Rahotanni sun nuna cewa matakin ya zo ne a daidai lokacin da ake ci gaba da shirye-shiryen babban zaɓen ƙasa mai zuwa, inda jam’iyyun siyasa ke ƙoƙarin tsara dabarun su domin samun nasara.








