Zanga-Zangar Iran: Jagoran Musulunci na ƙasar ya fadi matakin da za su ɗauka

Jagoran Juyin Juya Halin Musulunci na Iran ya bayyana cewa zanga-zangar da ’yan kasuwa suka gudanar sakamakon faɗuwar darajar kuɗin ƙasa zanga-zanga ce ta halatta, kuma suna da ’yancin yin ƙorafi kan halin da ake ciki.

Sai dai ya jaddada cewa ba abin yarda ba ne wani rukuni na ’yan haya na abokan gaba su fake a bayan masu zanga-zangar, suna rera taken adawa da ƙasar Iran da kuma Musulunci.

Jagoran ya bambanta tsakanin zanga-zanga da tarzoma, yana mai cewa zanga-zanga abu ne dabam da tayar da hankali. Ya ce gwamnati za ta shiga tattaunawa da masu zanga-zangar, amma waɗanda ke tayar da tarzoma za a mayar da su inda ya dace.

Ya kuma yi gargaɗin cewa dole ne a fahimci makircin abokan gaba, domin a cewarsa ba sa hutawa, kuma suna amfani da kowace dama da suka samu.

A ƙarshe, Jagoran Iran ya bayyana cewa ƙasar ba za ta ja da baya ba a gaban abokan gaba, yana mai cewa da dogaro ga Allah da goyon bayan al’umma, za su tilasta wa maƙiya durƙusawa.

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
guest
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments