Hukumar kula da zirgazirgar ababan hawa ta jihar Kano wato (Karota) ta bayyana shirin ta na aiki ba sani ba sabo wajen dakume duk wadan su masu karya dokokin tuki a lokacin bukukuwan Sallah mai zuwa a fadin titunan jahar.
Daga Kabir A. Dukawa
Shugaban Hukumar Dacta Baffa Babba Dan’agundi, shine ya bayyana hakan ta bakin Jamiin hulda da jama’a na hukumar KAROTA Nabilsi Abubakar Kofar Na’isa, inda yace, hukumar ta tanadi Jami’anta na musamman sama da 2000, wadanda zasu tabbatar da al,umma sun bi doka tare kame duk wadansu masu kunen kashi wajen karya dokoki a kan tituna lokacin bukukuwan Sallah a birnin jahar Kano.
Dan’agundi ya gargadi iyayen yara da su zamo masu tsawatar wa yayan su musamman masu ganganci da ababen hawa a kan tituna a lokacin gudanar da bikin Sallah.
Daga karshe ya shawarci direbobi da su zamo masu bin dukkanin dokokin tuki dana titi domin kare faruwar hadura a lokacin bukukuwan Sallah baki daya.