Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya kaddamar da hukumar yaki da cutar zazzabin cizon sauro ta kasa (NMEC) a wani babban taron da ya gudana a dakin taro na fadar shugaban kasa dake Aso-Rock Villa.
Bayan kaddamar da hukumar ya Mika jogorancin ta ga babbab atttajirin nan na Africa wato Aloko Dangote, inda a take ya karbi nauyin jan ragamar shugabancin majalisar.
Dangote ya ce sabon mukamin ya yi daidai da matsayinsa na Jakadan Najeriya a kan cutar zazzabin cizon sauro, da rawar da yake takawa a hukumar yaki da cutar zazzabin cizon sauro ta duniya, da kuma aikin da gidauniyarsa ta Aliko Dangote ke yi.wanda shine zai tara kamfanoni masu zaman kansu don tallafawa yaki da cutar zazzabin cizon sauro a Najeriya dama kasashen Afirka baki daya.
Yayin kaddamar da majalisar mai wakilai 16, shugaba Buhari ya yi hasashen cewa, idan aka samu nasarar aiwatar da ajandar majalisar da kuma tanadin kasafin kudin da aka yi kiyasin tattalin arzikin kasar zai ceto Najeriya da kimanin Naira biliyan 687 a shekarar 2022 da kuma Naira tiriliyan 2 nan da shekarar 2030.
Shugaban ya shaidawa majalisar cewa, baya ga inganta rayuwa, lafiya da walwalar ‘yan Najeriya, tsarin hadin gwiwa na magance cutar zazzabin cizon sauro na da fa’ida ga lafiyar al’umma da kuma zamantakewar tattalin arziki ga Nijeriya.
“Saboda haka bukin rantsar da mu a yau zai tabbatar da cewa kawar da cutar zazzabin cizon sauro ya ci gaba da kasancewa a gaba a ajandanmu, tare da jajircewar siyasa daga shugabanni a dukkan matakai. Bugu da kari, kwamitin yaki da cutar zazzabin cizon sauro zai samar da wani dandali na neman karin kudade don kare da dorewar ci gaban da kasarmu ta samu, tare da dora mu kan hanyar kawo karshen cutar zazzabin cizon sauro da kyau,” in ji shugaban.
Yayin da yake nuna damuwar cewa cutar da ta dade tana ci gaba da zama babban kalubalen kiwon lafiyar al’umma a Najeriya, shugaban ya yi misali da rahoton Hukumar Lafiya ta Duniya (WHO) na shekarar 2021, inda ya nuna cewa Najeriya kadai ce ke da kashi 27 cikin 100 na masu kamuwa da cutar zazzabin cizon sauro da kashi 32 cikin 100. na mutuwa a duniya.
Akan zabin da aka yiwa Dangote a matsayin shugaban majalisar, Buhari ya bayyana cewa, ya kasance bisa la’akari da tarihi da kuma kishin attajirin da ya fi kowa kudi a Afirka wajen tallafa wa kudirorin da suka shafi kiwon lafiya daban-daban kamar cutar shan inna da karfafa tsarin kiwon lafiya a matakin farko.
Ya kuma bayyana kwarin gwiwarsa na cewa Dangote zai kawo gagarumin sauyi da nasarorin da ya samu domin taimakawa kasar nan wajen cimma burinta na kawar da cutar zazzabin cizon sauro, ya kuma kara da cewa an zabo wasu manyan mutane, wadanda su ma suka taka rawar gani a kowane fanni na rayuwa da za su yi aiki a majalisar.
Ya kara da cewa, zama mambobin majalisar na nuni da kudirin gwamnati na rage radadin cutar zazzabin cizon sauro a Najeriya, zuwa matakin da baya shafar lafiyar al’umma.