Yadda Radio Najeriya Pyramid ta gudanar da bikin cika shekaru 18 da kafuwa

AKSAM MEDIA ta taya RADIO NIGERIA PYRAMID Kano murnar cika shekaru 18, da kafuwa

Daga Kabiru A. Dukawa

Ma’aikatan AKSAM MEDIA CONCEPT, sun kai ziyarar taya murna ga gidan RADIO NIGERIA PYRAMID Kano, bisa cika shekaru 18, da kafuwa tare yada shirye – shirye, masu Ilimantar wa da Fadakar wa da Wa’azantar wa da kuma Nishadantar wa ga al’umma a jahar Kano da makobtan jihar.

AKSAM ta kai ziyarar ne a ranar Litinin 21, ga Watan Mayu, 2022. harabar gidan rediyon dake no. 3, a kan titin Audu Bako Way, kusa da Magwan a birnin Kano ta Dabo.

A yayin ziyarar Ma’aikatan na AKSAM, sun yaba wa shugaban gidan rediyon na PYRAMID, Malam Abba Bashir bisa yadda yake ba wa Dalibai masu koyan aikin Jarida cikakkiyar dama na samun kware wa a aikin ba tare da nuna wani wariya ba.

San nan kuma, Ma’aikatan karkashin jagorancin shugaban su Abubakar Suleman Gwammaja, sun gode shugaba kuma Uba ga wannan media ta AKSAM Adamu Dabo, bisa yadda yake bata dukkanin gudun mawar da ta kamata wajen ciyar da ita gaba.

Daga karshe sun mika wa shugaban na gidan rediyon Bana na taya murnar shekaru 18, da gidan rediyo yayi yana yada shirye – shirye.

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
guest
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments