Ana so kowanna mutum ya saka a ransa cewa babu tabbataccen Abu Sai nagartacce, Don haka kayi du mai yuwuwa Ka zama nagartacce.
Abubuwan da zasu baka dama Ka zama Nagartacce
A) Ka lazimci zama da mutanen kirki, Kuma Ka rika koyon Abubuwan da Ka Gani mai kyau a tare da su.
B) Ka kauracewa zama da mutanen kawai Ka rika addua Allah ya saka hijabi tsakanin Ka da su.
C) Ka horas da gabobin ka akan aikin alkhairi wanda annabi Muhammad s. A w ya koyar
Ka ka rika neman gaskiya a koda yaushe idan ta samu kar ka duba agurin wa ka sameta Ka duba wanda yazo da ita domin “Gaskiyar addinin Musulumci tana rarrabe a cikin kungiyoyin addinin” Farfesa Makari.