Wata mata ta shiga hanun Yan sanda bisa laifin garkuwa da kanta

Wata matar aure mai juna biyu, Jamila Ardo, ta shiga hannun hukuma kan zargin laifin garkuwa da kanta kuma ta karbi kudin fansa hannun masoyinta.

 Jamila, wacce yar Wuru Jobe ce a karamar hukumar Yola ta kudu ta jihar Adanawa ta sace kanta kuma ta karbi kudin  fansan naira miliyan biyu a hannun Mallam Ahmed Adamu, wani masoyinta dake Abuja.
 Ana zargin matar da hada kai da wani mai suna Abdulaziz wajen garkuwa da kanta don damfarar wani mai sonta.
Rahoton yace tayi amfani da kudin wajen sayen gida. Matar da Adamu sun fara soyayya ne ta Facebook, amma bai san matar aure bace.
Jaridar Punch ta tattaro cewa duk da cewa basu taba haduwa ba, amma dare daya wani Abdulaziz ya kira masoyin yace masa an yi garkuwa da ita kuma an nemi kudin fansa.
 Saurayin nata na Facebook mai suna Adamu cikin tausayi ya biya kudin fansar ta asusun banki mai suna, Amina Mohammed.
Rahoton yan sanda yace: “Bayan karban kudin, ta fadawa Adamu cewa masu garkuwa da mutanen sun sake ta.” “A lokacin Adamu ya fara zargi kuma ya shigar da kara ofishin yan sanda ranar 16 ga Nuwamba, 2021.”
Bayan nutsa bincike da Jami’an tsaro suka you a yanzu haka sun damke mai asusun bankin da aka tura kudin kuma aka bibiyeta aka kamota.
Daga baya aka gurfanar da ita gaban kotun majistare dake Yola kan laifin garkuwa da mutane. Lauyan Jamila,  Crowealth ya bukaci kotu ta baiwa Jamila damar ganin Likiti saboda juna biyun da take dauke da shi.
 Alkalin, Digil, ya bada belin kuma ya dage karar zuwa ranar 10 ga Maris, 2022, amma yace a garkame sauran.
0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
guest
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments