Wasu gwamnonin APC sun lashi takobin baiwa Tinubu Matsala a jihohin su

An ba kowane Gwamna dama ya kawo sunayen wadanda za a sa a kwamitin takarar Bola Tinubu Ko da sunaye suka fito, sai ga wasu Gwamnonin APC suna kukan ‘Dan takaran ya yi watsi da alkawarin da yayi musu

A yanzu haka Sabani a iya cewa ya yi kamari kasancewar an samu Gwamnonin da ke yi wa Tinubu barazanar kin goyon bayan takararsa

Wasu daga cikin gwamnonin jam’iyyar APC mai mulki, sun yi barazanar kawowa takarar ta Asiwaju Bola Tinubu cikas a jihohinsu muddin zabe yazo.

Wani rahoto na musamman da muka samu daga Premium Times a ranar Litinin, ya bayyana cewa ‘yan kungiyar PGF suna jin haushin Bola Tinubu.

Gwamnonin APC sun fusata ne a kan yadda jam’iyya da ‘dan takararta suka yi watsi da sunayen da suka bada na wadanda za a sa a kwamitin kamfe.

Gwamnonin sun ce sun aiko da sunayen mutanen su na APC biyar biyar da za su shiga cikin kwamitin jam’iyyar na yakin neman zaben shugaban kasa, amma sai magana ta canza daga baya lamarin da ya basu mmamaki shi ne, da aka fitar da jerin sunayen ‘yan kwamitin kamfe, sai suka ga an yi watsi da sunayen da suka gabatar.

Kwamitin yakin neman zaben Bola Tinubu sun yi wannan ne ba tare da sanin gwamnonin ba. Wannan ya jawo aka yi ta kai wa APC da PGF korafi

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
guest
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments