Jawabin Meloni bayan samun nasarar zabar ta a matsayin mace firaminita ta farko a Italiya

Meloni wadda ke jawabi a birnin Rome, bayan da da sakamakon da ke fitowa ya nuna cewa jam’iyyarta ta lashe kaso 26 na kuri’un da aka kada, ta ce za ta bada jagoranci ga ilahirin ‘yan kasar.

Sakamakon ya nuna cewa akalla mutum 1 cikin 4 na wadanda suka kada kuri’a a zaben na Lahadi ya kada wa jam’iyyar Brothers of Italy.

Ko da yake cikakken sakamako bai fito a hukumance ba sai zuwa yammacin Litinin din nan, manyan abokan hamayyarta sun bada kai bori ya hau, inda suka ce rana ta bace musu.

Meloni ta yi ta kasancewa  a kan gaba a kuri’ar jin ra’ayin jama’a tun bayan da Firaminista Mario Draghi ya sanar da yin wani zabe a watan Yuli, bayan rugujewar gwamnatinsa ta hadaka.

Sakonnin taya murna dai sun fara shigowa daga abokanta a nahiyar Turai, inda Fira ministan Poland Mateusz Morawiecki da jam’iyya mai tsatsauran ra’ayi na Spain da sauransu duk suka aike da sakonni.

Italiya ta yi kaurin suna wajen yawan sauyin gwamnati, inda aka samu gwamnatoci kusan 70 a kasar tun daga shekarar 1946.

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
guest
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments