Tun bayan kifar da Gwamnatin Bashar Al-Asad al’ummar Syria na kukan Gaza Samun Daidaitaccen Tsarin Tsaro

Shekara guda bayan kifar da mulkin Bashar al-Assad, ƙasar Syria na ci gaba da fuskantar manyan ƙalubale da dama. Daga cikin muhimman abubuwan da sabuwar gwamnati ta sa a gaba akwai sake gina rundunar sojojin ƙasa da kuma jami’an tsaro na ƙasa.

Tsawon shekaru da dama, tsarin tsaro da rundunar sojojin Syria sun kasance, a ganin mutane da yawa, wata runduna mai tsauri da ake amfani da ita wajen kare mulkin gwamnati tare da murkushe masu adawa da ita.

Yanzu dai ana kokarin sake gina rundunar sojoji tare da kafa sabon tsari (dokar aiki) wanda biyayya za ta kasance ga ƙasa baki ɗaya, ba ga wani mutum ko ƙungiya ba.
“Mun fara aikin sake fasalin sojojinmu da rundunar tsaro… kuma muna biyan bukatar wannan lokaci ta hanyar gina rundunar sojoji da Syria ta cancanta a matsayinta na ƙasa, wato rundunar da za ta wakilci Syria kuma ta kasance mai iya fuskantar ƙalubalen da ke gabanta,” in ji Ministan Tsaro Murhaf Abu Qasra yayin wani biki na yaye sojoji daga makarantar horas da sojoji a birnin Aleppo.

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
guest
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments