Jami’an Hukumar KAROTA sun kama wasu matasa biyu da ake zargin sace wayar Fasinja a cikin Baburin Adaidaita Sahu.
Waɗanda ake zargi da satar wayar sun haɗa da Ibrahim Sale Rijiyar Lemo da Abubakar Salisu Zoo Road bisa zargin sace wayar fasinjan Adaidaita Sahu Hassan Muhammad Sani
Wanda aka daukewar wayar Hassan Muhammad, ya ce lokacin da ya tsayar da su ya neme su kai shi Bata daga shatale-talen gatar Dangi bayan sun ɗauke masa wayarsa sai suka ce ba inda ya bayyana baza su je ba.
Hassan Muhammad, ya kara da cewa bayan da ya sauka ne sai ya fahimci sun ɗauke masa, a inda ya nemi taimakon jami’an KAROTA da ke aiki a wannan wuri.
Lokacin da suke hannun Jami’an Karotar matasan sun ce, fiye da shekara guda suna aikata wannan mummunar ta’adar ta ɗaukar Fasinja a cikin Baburin Adaidaita Sahu mai lambar KAROTA KRY 1539.
An sami wayoyi iri daban-daban a hannun matasan tare da nau’in kayan shaye-shaye
Shugaban Hukumar ta KAROTA Hon. Baffa Babba Ɗan’agundi na ƙara kira ga al’umma da su cigaba da sa ido a duk lokacin da za su hau Baburin Adaidaita Sahu tare da lura da Koriyar lambar jiki da irin mutanen da suke ciki domin gujewa faɗawa hannun ɓata-gari.
Hukumar ta miƙa su hannun Rundunar ‘Yansanda ta jihar Kano domin ta faɗaɗa bincike tare da gurfanar dasu a gaban Shari’a