Duk a kokarin ganin matasa sun kauracewa zaman bakin layi ne yasa dan majalisar tarayya mai wakiltar funtuwa da dandumen jihar katsina kuma zababban dan takarar sanata a jam’iyyar APC muntari dandutse lasar takobin kakkabe wannan zama ta hanyar horas da matasa maza da mata 3000 sana’o’in dogaro da kai
Daga wakilin aksammedia B.imam
Dandutse ya ayyana wannan alkawari tin lokacin da yake gudanar da yakin neman zabe inda ya shaidawa al’ummar zai yaki da zaman kashe wando ta hanyar baiwa matasa maza da mata aikin yi da koyar dasu sana’o’in dogaro da kai
Ya kara tabbatarwa da hon.umar ya’u (abba ja )wannan aniya tasa a yayin wata zantawa da sukai inda ya ambata masa dalin sa na aiwatar da wannan aniya tasa a cewar dan takarar sanatan yace mun daura damarar hakan ne la’akari da yadda ake fama da rashin aikin yi rasa aikin yi kuwa shine musabban jefa jihar ga halin rashin tsaro wannan dalili ne yasa na daura damara domin kakkabe cigaban faruwar hakan
A karshe yayi kira ga al’ummar jihar katsina dama kasa baki daya da’a dukufa wajan addu’ar nemawa jihar dama kasa biki daya kasancewa cikin zaman lafiya da kwanciyar hankali