Ministan Harkokin Wajen Iran, Ya Fitar da sabuwar sanarwa ga Amurka da kawayen ta

Ministan Harkokin Wajen Iran Ya sake Fitar da sabuwar sanarwa ga Amurka da kewaye ta

A cikin wani sharhi da aka wallafa a jaridar Wall Street Journal, Abbas Araghchi, ya bayyana cewa Tehran ta sha zaɓar hanyar zaman lafiya maimakon fuskantar rikici, tare da jaddada cewa ƙasar a shirye take ta cimma yarjejeniya ta adalci.

Araghchi ya yi gargadin cewa matakan tsokana da Amurka ke ɗauka—tun daga takunkumin tattalin arziki zuwa barazanar amfani da ƙarfin soja—ba su yi nasara ba a kan Iran. Ya ce irin waɗannan matakai ba za su tilasta wa Tehran sauya matsayinta ba, yana mai kira ga warware matsaloli ta hanyar tattaunawa da mutunta juna.

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
guest
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments