A shirye Chelsea take domin ta bar ɗan wasan gaba na ƙasar Belgium mai shekara 29 Romelu Lukaku ya ci gaba da zama a Inter Milan har zuwa kaka mai zuwa a matsayin aro kafin ta sayar da shi. (Gazzetta dello Sport, via Mirror)
Crystal Palace na tunanin sayen ɗan wasan gaban Blackburn da Chile mai shekara 23 Brereton Diaz. (Sun)
A ɗayan ɓangaren kuwa Sevilla ta sha gaban Everton da Leeds da Fulham a ƙoƙarin da ake yi na sayen Brereton Diaz a watan Janairu. (Football Insider)
Akwai yiwuwar Arsenal za ta sayi ɗan wasan baya na Faransa Evan Ndicka mai shekara 23 daga Eintracht Frankfurt a watan Janairu. (Sta ndard)
AC Milan na sha’awar ɗaukar ɗan wasan Chelsea da Albania mai shekara 21 Armando Broja. (Standard)
Arsenal da Manchester City da Juventus da Roma da AC Milan duk na sha’awar sayen ɗan wasan tsakiyar Celtic da Irelan Rocco Vata mai shekara 17. (Tuttomercatoweb – in Italian)
Ɗan wasan gaban Manchester United Christiano Ronaldo na fuskantar biyan diyyar fam miliyan ɗaya wanda kulob ɗin ya ƙaƙaba masa bayan ya bar wasa ana tsaka da gumurzu da Tottenham. (Star)
Akwai yiwuwar United za ta bar ɗan wasan mai shekara 37 ya tafi a kyauta a watan Janairu idan ba a samu mai sayen shi ba. (inews)
Real Madrid da Paris St-Germain da Manchester United duk sun tura wakilai domin sa ido kan ɗan wasan Napoli da Georgia Khvicha Kvaratskhelia mai shekara 21. (90min)
Sai dai ana sa ran ɗan wasan tsakiya na Slovakia Stanislav Lobotka mai shekara 27 zai saka hannu a wata sabuwar yarjejeniya da Napoli duk da cewa Arsenal da Liverpool da Tottenham na son shi. (90min)
Arsenal ta so ta sayi ɗan wasan bayan Najeriya Calvin Bassey mai shekara 22 daga Rangers a wannan kakar kafin ya tafi Ajax. (Own Goa l Nigeria)