Shugaban kwamitin amintattu na jam’iyar PDP, Walid Jibrin ya bukaci jam’iyar PDP ta sake duba fasalin rabon mukaiman da jam’iyar tayi.
Jibrin ya bukaci hakan ne a yayi da yake zantawa da Gidansa tabijin na channel inda yace jam’iyar bata yi duba na tsanaki ba a yayin Raba mukaman.
Yace bai kyautu jam’iyar ta fito da shugaban ta daga Arewa ba kuma Dan takarar shugaban kasar ta daga Arewa dadin dadawa shugaban kwamitin amintattu Shima daga Arewa
Ya ce a shirye yake ya mika mukamin sa na shugaban kwamitin amintattu ga yankin kudancin Kasar nan in har hakan zai Kawo masalaha a jam’iyar.