An yi kira ga Gwamnatin jihar Kano da hukumar dake kula da gyara gyaren hanyoyi ta jihar (KARMA) da su kawowa titin da ya tashi Daga railway zuwa roundabout din AA Rano zuwa titin Audu Bako way, daukin gaggawa duba da yadda alumma suke samun cokoson ababen hawa a lokuta daban daban, musamman masu gudanar da kasuwancinsu a yankunan.
Shugaban kungiyar matasan kasuwar masu magunguna kuma, mai rajin ci gaban alummar jihar Kano, Alh mamuda Zangon Kabo ne yayi wannan kiran dangane da yadda alumma suke tsintar Kansu a ciki, musamman,masu yawan bin hayoyin Yau da kullum.
Ya ce,kamata yayi Wanda alhakin gyaran ya rataya akansu suyi duba na tsanaki domin sanin gyaran da za,a yiwa wadannan hanyoyi domin lalacewar ta yi mutukar ta,azzara.
Yace, rashin magudanan Ruwa yana da ya Daga cikin abubuwan da yake haifar da yawan ambaliyar Ruwa a yankunan da dama a fadin jihar,inda ya bukaci alumma da su kasance suna aikin gayya da share magudanan Ruwa domin kaucewa yawan ambaliyar Ruwa da ta yi yawa a halin yanzu.
Haka zalika, ya yabawa Gwamnatin jihar Kano, bisa kafa kwamatin da zai rika lura da gyaran magudanan Ruwa da guraren da suka yi gine gine ba bisa kaidaba musamman a hanyoyin magudanan Ruwa, Wanda yin haka na Daga cikin abubuwan dake haifar da Ambaliyar Ruwa da zubewar gine gine a lokuta daban daban.
Ya shawarci masu hannu da shuni da su ji gaba da tallafawa Matasa a unguwanni domin share magudanan Ruwa da yin ayyukan gayya don zai taimaka kwarai kaucewa yawan ambaliyar Ruwa.
(Ibrahim Sani gama)