Iran ta ce tana yaƙi ne da fannoni guda hudu

Amurka, wadda ta kakaba takunkumin tattalin arziki mafi tsauri a tarihin bil’adama.

Isra’ila, ta hanyar ayyukan leken asiri da na soji na Mossad, ciki har da lalata tsaro da daukar hayar ‘yan haya (mercenaries).
Kungiyoyin ta’addanci masu alaka da ISIS da sauran ‘yan tsattsauran ra’ayin Takfiri, wadanda wasu kasashen Musulmi ke mara wa baya.

Kungiyoyin da ke da alaka da tsohon mulkin Shah, wadanda suka tsere daga Iran a shekarar 1979, kuma yanzu suna neman dawo da bangaren Pahlavi kan mulki.

An bayyana cewa wannan gwagwarmaya ce mai wahala kuma mai fuskoki da dama, wadda gwamnatin Iran ke fuskanta tsawon fiye da shekaru 40, kuma a yau ta kai wani muhimmin matsayi mai hatsari.

Rahoton ya ce ana sane da cewa al’ummomin da ake zalunta a duniya, tare da ’yan’uwa maza da mata a sassa daban-daban na duniya, suna kallon abin da ke faruwa a Iran cikin damuwa, sakamakon farfagandar Yamma da Isra’ila. Sai dai an jaddada cewa, da goyon bayan al’ummar Iran, jarumtakar dakarun tsaro, da taimakon Allah, za a yi nasara a wannan gwagwarmaya.

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
guest
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments