Biyo bayan tsallake rijiya da baya da Mataimakin gwamnan jihar Kebbi yayi a jiya laraba yanzu haka masana a harkar gudanar da mulki a Najeriya sun shiga today albarkacin bakin su.
By Hassan Umar Gwammaja
Lamarin kai harin ya faru ne inda Mataimakin Gwamnan jihar Kebbi, Kanal Samaila Yombe Dabai Mai Murabus, Ya Tsallake Rijiyar Da Baya
Bayan arangamar da tawagarsa ta yi da ‘yan ta’adda a garin Kanya da ke Karamar Hukumar Danko Wasagu a jihar ta Kebbi.
A zatawar Kanal Dabai da Radio Nigeria, ya bayyana yadda ‘yan ta’addan suka yiwa tawagar sa kwanton Bauna da kuma yadda tawagar tasa suka kubuta.
Sai dai sanata Shehu Sani yace lamarin akwai bukatar matsa kaimi wajan yakar Yan taaddan indai masu rike da madafun iko Basu tsira daga Kai harin Yan taaddan ba to babu Wanda zai tsira.