Rundunar yan sintiri ta vigilantee a jihar kano tare da Jami’an yan sanda da Sauran Jami’ai sun shirya tsaf don ganin anyi bukukuwan Sallah karama lafiya an gama lafiya.
Da yake zantawa da manema labarai a safiyar wannan rana Babban kwamandan Rundunar ta Vigilantee na jihar kano, Alhaji Shehu Rabi’u yace tuni Jami’an vigilantee na farin kaya suka fara bazuwa Cikin loko da sako a dukkannin guraren da akasan mafakar bata gari ce domin bayar da bayanan sirri don daukar matakin da ya dace, ya kara da cewar, duk wanda aka kama babu shakka zai fuskanci fushin Hukuma.
Daga nan yayi kira ga Al’ummar jihar kano da makobtan jihohin kano musamman masu zuwa yawon sallah da kuma ziyarar dangi dasu kasance masu Kula da sanya idanu akan kananan yara don gudun bacewar su cikin rububi.
A karshe ya yabawa gwamnatin kano wajen gudummawar da take baiwa Jama’ar jihar ta fannin tsaron rayuka da dukiyoyin Al’umma musamman Kwamishinan kananan hukumomi Hon Murtala Sule Garo da Shugaban dake kula da ayyuka na musamman na fadar gwamnatin kano kanal malami mai ritaya tare da yan Jaridu ta fannin wayar da kan Jama’a a lokuta daban daban.