Tsohon ministan harkokin Niger Delta, Godswill Akpabio ya bayyana cewa zai tunkari kotun koli domin daukaka kara a hukuncin kotun daukaka kara
Ya bayyana cewa a matsayinsa na lauya, yana jiran kwafin shari’arsu sannan su san abinda ya dace su yi amma zasu je har kotun karshe
Akpabio yayi kira ga magoya bayansa, mambobin APC da ‘yan mazabarsa da su kwantar da hankali har zuwa lokacin da za a yanke hukuncin karshe