Farasa ta kaddamar da hare-hare a kasar Nijar

Jirage marasa matuka na Faransa sun kashe mayaka masu ikirarin jihadi 40 a farkon wannan makon a yayin da suke tafiya bisa babura a kusa da iyakar Nijar da Burkina Faso, kamar yadda rundunar sojin Faransa ta sanar.

A wata sanarwa, sojin Faransa ta  bayyana hare haren a matsayin wata nasara da ta samo asali daga sabon salo da suka bijiro da shi a yakin da suke da ta’addanci a yankin Sahel na nahiyar Afrika.

Sanarwar  ta ce bayanan sirrin da aka samu daga sansanin sojin hadaka ta Barkhane sun tabbatar da cewa baburan da suka yi ayari mallakin wata kungiyar ta’addanci ne da ke da ke tafiya tsakanin Burkina Faso da Nijar.

Bayan wannan tabbacin ne dai rundunar Barhkane din da taimakon sojin Nijar suka yi ta luguden wuta a kan mahaya baburan, lamarin da ya yi sanadin mutuwar ‘yan ta’addan kusan 40.

Gwamnatin Nijar ta fitar da wata sanarwa da ke cewa an kashe ‘yan ta’addan ne  bayan da wani hari da suka kai ya yi sanadin mutuwar  jami’an tsaro 7 a kudu maso yamacin Nijar.

Bayan da gwamnatin Mali ta nuna ba ta bukatar dakarun Faransa a kasarta, Nijar ta zama abokiya ta kud-da-kud da  Faransa a yankin Sahel.

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
guest
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments