China ta Kafa Tarihi Bayan kammala Wani babban aiki a ƙarƙashin Ruwa

China ta kammala gina wata babbar hanyar jirgin ƙasa ta karkashin ruwa cikin ƙasa da watanni uku kacal, lamarin da ya kafa sabon tarihi wajen saurin aiwatar da manyan ayyukan gine-gine.

An yi amfani da fasahar zamani ta immersed-tube, inda aka hada sassan hanyar a gaba sannan aka rufe su a karkashin ruwa, abin da ya kauce wa matsalolin hako kasa na gargajiya tare da ba da damar ci gaba da zirga-zirga ba tare da tangarda ba.

Ramin hanyar na taimakawa rage cunkoson ababen hawa a yankunan gabar teku masu yawan jama’a, tare da inganta alaka tsakanin yankuna. Hakan ya nuna kwarewar kasar Sin a fannin daidaito da ingantaccen tsari na aiki, tare da zama abin koyi wajen bunkasa ababen more rayuwa na zamani cikin sauri a birane.

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
guest
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments