A yau Alhamis shugaba Xi Jinping na kasar Sin, da takwaransa na kasar Congo Kinshasa Félix-Antoine Tshisekedi Tshilombo, suka aikewa juna sakon murnar cika shekaru 50 da dora huldar da ke tsakanin kasashen 2 kan hanyar da ta dace.
A cikin sakonsa, Xi ya nuna cewa, a rabin karnin da ya gabata, kasashen 2 sun raya hulda a tsakaninsu yadda ya kamata, sun kuma rika zurfafa dankon zumunci a tsakaninsu. A shekarun baya, kasashen biyu sun kafa huldar abokantaka bisa manyan tsare-tsare, kuma hadin gwiwarsu ya haifar da sakamako mai yawa, kuma hakan ya amfani al’ummomin kasashen biyu. Xi ya kara da cewa, yana dora muhimmanci kan raya dangantaka a tsakanin kasar Sin da kasar Congo Kinshasa.
Yace yana son yin kokari tare da shugaba Félix-Antoine Tshisekedi Tshilombo, wajen yin amfani da damar cika shekaru 50 da dora huldar kasashen biyu a kan hanyar da ta dace, domin zurfafa amincewar juna ta fuskar siyasa, da inganta hadin gwiwarsu a fannin aiwatar da shawarar “ziri daya da hanya daya”, da kuma bude sabon babi na bunkasar huldar da ke tsakanin kasashen biyu.
A nasa bangaren, Félix-Antoine Tshisekedi Tshilombo ya ce, a cikin shekaru 50 da suka wuce, kasarsa da Sin sun bunkasa hulda a tsakaninsu yadda ya kamata ba tare da kasala ba. Yana kuma fatan kara zurfafa dankon zumunci a tsakanin kasashen biyu, da kara azama kan samun sabbin sakamako wajen bunkasar huldar abokantaka a tsakanin kasashen biyu bisa manyan tsare-tsare, a kokarin kawo wa jama’ar kasashen biyu alheri.