Sakamakon matakin da babban bankin Najeriya ya dauka na sauya fasalin wasu takardun kudin kasar, an umarci al’ummar kasar da su mayar da tsoffin kudaden da za a sauya zuwa banki.
CBN, ya ce idan mutane suka mayar da kudaden ba tare da bata lokaci ba, to za su iya samun musayar kudinsu a kan kari.
A ranar Laraba ne babban bankin Najeriyar ya sanar da matakin sauya fasalin kudin kasar daga takardar naira 100 zuwa 1000, in da ya buƙaci masu kuɗi a hannu su mayar da su bankuna cikin ƙasa da kwana 50.
Kazalika CBN din, ya ce ce sabbin kudaden da za a samar za su fara yawo a hannun mutane daga ranar 15 ga watan Disambar 2022, sannan kuma za a ci gaba da amfani da tsofaffin kudaden har nan da ranar 31 ga watan Janairun 2023.