Gwamnatin jahar Bauchi ta saka dokar hana fita waje na tsawon sa’o’i 24, a karamar hukumar Yelwa, Tsakani, Lushi, Kagadana da kuma Birshi, a sakamakon barkewar rikici a yanki.
Daga Kabiru A. Dukawa
Shugaban ma’aikata na jahar Dacta Aminu Hassan Gamawa ne ya sanar da haka ga manema labarai, inda yace Gwamnati tayi haka ne a kokarin ta na samar da zaman lafiya a yankunan.
Sanarwar tace, an saka dokar ne a sakamakon Wadansu bata gari da suka tada rikici tare da daukar dokar a hannun su wajen fasa shagunan mutane da kone konen Motoci da Gidaje dukiyoyin al’umma da kuma sace sace a yankunan.
Daga karshe Gwamnatin jahar ta gode wa hukumomin tsaro da Sarakunan gargajiya da Malaman addinai da kuma sauran al’umma masu kokarin kiyaye ka’idoji da dokoki da aka sanya a kowanna lokaci a jahar.